On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Atiku Ya Bukaci Yin Sabuwar Maja Domin Tunkarar APC

Tsohon mataimakin shugaban kasa , Atiku Abubakar ya ce yana da yakinin cewar hadewar jam’iyyun hamaiyya wuri daya zai temaka wajen kafa wata babbar jam’iyyar da zata kalubalanci jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

Atiku wanda  ya kasance dan takarar shugaban kasa a zaben da  ya gabata karkashin jam’iyyar  PDP, ya baiyana haka ne a Abuja  a jiya a lokacin da ya karbi bakuncin yan gudanarwar majalisar bada shawarwari a tsakanin jam’iyyu.

Atiku  ya koka  ka salon  takun jam’iyyar APC a kasar nan  wadda take neman komawa  salon tsarin  mulkin  kama  karya, a saboda  haka ne ya yi kira  ga  yan kungiyar  dasu bada shawarar yadda za’a kafa  wata  babbar jam’iyayr guda  daya  domin Maja.

Yan kungiyar  sun kai ziyarar ne  bisa jagorancin  shugabansu na  kasa  Yabagi Sani.