On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Atiku Ya Kai Zaiyarar Jajanatawa Kan Ambaliyar Ruwa A Jihar Jigawa Tare Da Bada Tallafin Kudi Naira Milliyan 50

‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.

Atiku ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr Nuhu Muhammad Sunusi a fadarsa,  Atiku ya ce dalilin da ya sa ya kai ziyarar shi ne don jajanta wa jihar da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa bisa barnar da al'amarin ya jawowa  ihar.

‘Dan takarar shugaban kasar ya ziyarci sarakunan Hadejia da Dutse yayin ziyarar a jiya a ranar asabar.

More from Labarai