On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Atiku Ya Kaucewa Alkawarin Neman Lafiya A Gida Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa - 2023

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ki amincewa ya bada tabbacin yin amfani da Asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya na Najeriya wajen duba lafiyarsa idan ya zama shugaban kasa.

Atiku yace cibiyoyin kiwon lafiyar Najeriya ba zasu iya kula da  lafiyarsa ba, amma a shirye yake ya inganta bangaren idan aka zabe shi.

Ya kuma yi alkawarin bayyana halin lafiyarsa idan bukatar hakan ta taso.

Atiku ya bayyana haka ne tare da takwarorinsa na jam’iyyar NNPP da Labour, Rabiu Kwankwaso da kuma Peter Obi a lokacin taron tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa da gidan Talabijin na ARISE ya shirya.

Kwankwaso da Obi sun tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa za su yi amfani da Asibitocin  kasar idan aka zabe su kuma a shirye suke su bayyana halin lafiyarsu.

Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC shine kawai dan takarar da aka gayyata da bai halarci taron ba.

Hakan na zuwa ne yayinda Jam'iyar PDP ta yi zargin cewa ziyarar da ‘Dan takarar  shugaban kasa  na jam’iyyar APC Bola Tinubu ya tafi kasar waje, wata dabara ce ta kaucewa muhawarar ‘yan shugaban kasa da  gidan talabijin na Arise ya shirya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, daraktan yada labarai  na  yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bayo Onanuga, yace ya yi matukar mamaki ganin yadda gidan Talbijin din ya cigaba da yada halartar dan takarar duk da cewa a baya ya ce ba zai halarci taron ba.

Da take  mayar da martani, tawagar yakin neman zaben shugaban kasa ta  Atiku da Okowa ta dage cewa Tinubu ya fice daga Najeriya domin kaucewa halartar muhawarar ta gidan Talabijin.