On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kungiyar YOSPIS Ta Shawarci Abba Ya Ayyana Dokar Ta Baci Akan Matsalar Kwacen Waya A Kano

Kungiyar matasa mai zaman kanta ta dake rajin yaki da cututtuka masu yaduwa da matsalolin al’umma YOSPIS, na kira ga zababben gwamnan jihar Kano mai jiran gadon Engr. Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar ta-baci a kan Annobar kwacen  waya ta hanyar kafa wani kwamitin kwarta kwana da zai yi aiki tare da ‘yan sanda da bangaren  shari’a domin gudanar da bincike cikin gaggawa, tare da gurfanar da masu laifi a gaban shari’a.

Babbar Darakta, YOSPIS Zainab Nasir Ahmad wadda ta yi wannan kiran a taron manema labarai, ta koka kan yadda barayin waya suka farwa mutane da dama har wasu suka mutu, al’amarin da ya yi kamari a kwanan baya inda barayin ke kai hare-hare da rana suna kutsawa gidaje a cikin unguwanni  daban-daban.

Ta kara da cewa al’amarin yana da ban tsoro da ban tausayi ga tarihin jihar Kano, tana mai kira da a samar da kotu ta musamman da za ta kula da irin wadannan shari’o’i.

Ahmad ta kuma ba da shawarar cewa a sake nazari kan  dokokin da ake da su da suka shafi sace-sacen waya da kuma sabunta su don tabbatar da cewa sun magance yadda wannan mummunan laifi ke faruwa.