On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Babban Bankin Kasa Ya Ce Ba Zai Kara Wa'adin Yin Amfani Da Tsaffin Kudi Ba

Gwamnan Babban Bankin Kasa

Babban bankin kasa CBN, Ya ce babu wani karin wa’adin yin amfani da tsaffin takardun kudi na naira da aka sauyawa fasali da zai yi a nan gaba.

Yan Najeriya cikinsu hadda gwamnoni sun bukaci babban bankin kasar  ya tsawaita  wa’adin yin amfani da tsaffin kudin a saboda  karancin  sabbi da ake  fama dashi yanzu haka.

To sai dai kuma, Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele , Ya  ce  babu wani karin lokaci  na yin amfani da tsaffin kudin da bankin zai yi,bayan karewar  kwanakin goman da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dasu.

Gwamnan ya baiyana haka ne a birnin Ikko, yayin wani taron manema labarai da aka yi dashi a jiya, Inda ya roki jama’ar kasa dasu kara yin hakuri, tare  da baiyana cewar  ribar da za’a samu  game da tsarin  zai fi  kalubalen da ake  fuskanta.