On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Babban Bankin Najeriya CBN Zai Buga Sabbin Takardun Kudi Naira Milliyan 500 - Aisha

Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin kasa CBN, Aisha Ahmad ta ce an kammala shiri tsaf domin samar da sabbin takardun kudade naira miliyan dari 5 kuma za’a buga su nan ba da dadewa ba.

Ahmad ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin da ‘yan majalisar wakilai suka gayyaci tawagar bankin na CBN.

Da take tsokaci kan adadin takardun da ke zagayawa yanzu haka, mataimakiyar gwamnan bankin ta ce ba ta san nawa ne aka buga na sabbin takardun naira ba kawo yanzu.

Tace tana gudun kar ta bada  Alkaluma da ba haka suke ba.

‘Yan majalisar sun kuma yi wa Aisha Ahmad, da ke wakiltar Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, tambayoyi kan sabon tsarin cire kudi.

Tace  sabuwar dokar takaita hada-hadar tsabar kudi bata da alaka da wani dalilai na siyasa.