On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Babban Sakataren Kungiyar OPEC Muhammad Barkindo Ya Rasu

Marigayi Barkindo

Da Dumi-duminsa. Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Fitar da Mai ta Duniya OPEC, Muhammad Barkindo Ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a Daren Ranar Talata, kamar yadda shugaban kanfanin Mai na Kasa Mele Kyari ya baiyana haka a shafinsa na Twitter da safiyar yau Laraba.

Ya baiyaan cewa Marigayin ya rasu ne  da karfe 11 na Daren ranar Talata  5 ga watan Yulin 2022.

Koda a ranar Talatar  Marigayin ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin wata kwarya-kwaryar liyafar karramawa da aka shirya masa  ta sauka daga shugabancin Kungiyar OPEC a karshen watan yulin da muke ciki.

Ya baiyana cewa a yana haka an kan shirye-shiryen  sallatar Mamacin kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Marigayi Muhammad Barkindo ya shafe shekaru 6 yana jan ragamar kungiyar kasashe masu arzikin fitar da mai ta duniya OPEC

More from Labarai