On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Babu Kafar Yin Magudi A Zabukan Najeriya Na 2023 - Hukumar INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ce babu wata kafa da za a iya yin magudi a zaben 2023 a jihar Anambra.

Hukumar ta kuma bayar da tabbacin cewa  a shirye ta ke wajen  tabbatar da sahihin zabe na gaskiya da adalci, inda ta kara da cewa dole ne a kirga kuri’u da  jama’a suka kada domin yanzu za’ayi  zabe ba kamar yadda aka saba ba.

Kwamishiniyar zabe ta jihar Anambra, Dr. Queen-Elizabeth Agwu itace ta bayyana haka a lokacin da ta jagoranci ma’aikatan hukumar a jihar a ziyarar ban girma da suka kai wa basaraken gargajiya na Awka, Obi Gibson Nwosu.

Dr Agwu tace hukumar ta kai ziyara dukkannin kananan hukumomi ashirin da daya da ke jihar domin gabatar da rajistar masu kada kuri’a, tana mai bada tabbacin cewa nan ba da dadewa ba wadanda suka yi rajista daga watan Janairu na wannan shekara za su fara karbar katin zabe na dindindin.

More from Labarai