On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Babu Maganar Yin Hadaka Tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

HOTON KWANKWASO DA PETER OBI

A yanzu haka dai a iya cewa ta leko ta koma, kan maganar yuyuwar yin Hadaka tsakanin Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da kuma Dan Takarar shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda rahotanni suka tabbatar da cewa a halin yanzu babu wannan maganar.

Kusa a jam’iyyar  LP, Doyin Okupe  ya baiyana cewa babu wani shiri na yin Hadaka a tsakanin  jam’iyyun biyu kamar yadda wasu da dama ke tsammani.

A wata hira da aka yi da Sanata Kwankwaso a kwanan nan, Yace tabbas  da hadakar zata yuyuwa  shine abunda akafi so, to amma ba zai yadda  ya zama mataimakin  Peter Obi ba.

Kazalika rahotanni sun tabbatar da cewa  dukkanin mutanen biyu babu wanda yake son ya zama Dan Takarar Mataimakin shugaban kasa, A yayin da Doyin Okupe yace tuni aka binne  maganar   yuyuwar  yin Hadaka a tsakaninsu.

 

More from Labarai