On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Babu Ruwanku Da Bangarancin Siyasa - Gwamna Bala Na Jihar Bauchi Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi gargadi ga masu rike da sarautun gargajiya a jihar da su kaucewa siyasar bangaranci, yana mai cewa irin hakan zai zama sabawa tsarin gargajiya.

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a jawabinsa na karshen mako, jim kadan bayan mika sandar mulki ga mai martaba Sarkin Katagum na 12 da ke karamar hukumar Katagum, Alhaji Umar Faruk na  II.

Gwamna Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta amince da irin wannan hali ba, yana mai nuni da cewa duk da cewa su na kowa ne amma bai kamata su karkata a wani bangare ba.

Mohammed ya kuma yi gargadin cewa sakamakon rahotannin da ya samu na wasu sarakunan gargajiya a jihar da ake zargin suna da hannu a salwantar da wuraren kiwo da  dazuzzuka da burtalai a jihar, ba zai bar duk wanda aka samu da laifi ba.

More from Labarai