On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Babu Wata Tartibiyar Yarjejeniya Da Aka 'Kulla Tsakanin Kungiyar ASUU Da Gwamnatin Taraiyya

SANATA CHIRIS NGIGE

Gwamnatin Taraiyya ta baiyana cewa babu wata tartibiyar yarjejeniya da suka kulla tsakaninsu da kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Wadda a yanzu take dakon saka sa hannun shugaban kasa.

Ministan kwadago da samar da Guraban aiki,  Sanata Chiris Ngige ne  ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Mataimakin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ma’aikatar, Mister Oladije  Oshundun, wadda aka fitar jiya a Abuja.

Ministan Ngige ya baiyana cewa karin hasken ya zama wajibi, la’akari da wasu bayanai  da  Shugaban Kungiyar ASUU  Farfesa  Emmanuel Osodoke ke yiwa  yan Najeriya da kuma sauran shugabannin rassan  kungiyar, inda yake yin kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saka hannu kan yarjejeniyar da yayi ikirarin sun kulla tsakaninsu da gwamnati.

A cewar ministan kwadagon, Babu wata tartibiyar yarjejeniya  da aka kulla tsakanin kungiyar Malaman Jami’oin ta kasa da kuma gwamnati.