On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Bamu Gamsu Da Sharrudan Bada Lamunin Karatu Ga 'Yan Najeriya Ba - Shekarau

Tsohon Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau ya ga baiken Gwamnatin tarayya kan manufofinta na bada rancen karatu ga dalibai, inda ya ce sharudan sun yi tsauri ga talakawan Najeriya.

Da yake tsokaci kan batun ta cikin wata tattaunawa kai tsaye da  Arewa Radio, Shekarau ya bayyana cewa ana sa ran daliban za su tanadi  wadanda za su tsaya musu da suka mallaki makudan kudade  a asusun ajiyar su na banki.

A cewarsa, wannan tanadi da sauran su zai yi wahala ga mafi yawan daliban Najeriya su iya samun rancen.

Shekarau wanda kuma tsohon malamin makaranta ne, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba tare da kawar da wasu sharudda da ke cikin dokar don baiwa daliban Najeriya damar samun tallafin.

A bangaren tsaro kuwa, Malam Ibrahim Shakarau ya bayyana fargabar cewa idan ba a aiwatar yadda ya kamata ba,  'yan sandan jahohi na iya ta'azzara yanayin siyasa a jihohi da dama.

Sanata Shekarau ya kafa hujja da fargabar da ke tattare da tashe-tashen hankulan siyasa da ke ci gaba da tabarbarewa a wasu jihohin kasar nan, wadanda ake zargin ‘yan siyasa ne ke daukar nauyinsu da kuma tallata su.
Da yake jaddada goyon bayansa ga rundunar ‘yan sandan jihohi, Shekarau ya yi gargadin cewa kar 'kyale  jami’an su rike bindigogi da sauran makamai.

Tsohon sanatan na Kano ta tsakiya, ya bada shawarar samarwa 'yan sandan tsari irin na hukumar Hisbah ta Jihar Kano, wadda ke kula da al’amuran da suka shafi al’umma a lokacin da yake rike da kujerar gwamna.