On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Bankin Kasa Ya Kara Adadin Tsabar Kudi Da Mutum Zai Iya Cira A Rana

Bankin kasa CBN ya amince da Karin adadin tsabar kudi da Mutum ko ka kanfanoni zasu iya cira a rana zuwa mako.

Daga yanzu bankin ya ce Mutum zai iya cirar naira Dubu 500 a mako Wanda ya kama Dubu 100 ke nan a rana ,Yayin da kanfanoni zasu iya cirar naira milyan 5 a mako Wanda ya kama naira milyan 1 ke nan a rana.

Bankin Kasa ya ce ya dauki matakin ne bayan Shawarar da ya samu daga masu ruwa da tsaki.

A baya dai Bankin kasa ya ce daga Ranar 9 ga watan janairun 2023 Adadin kudin da Mutum zai iya cira daga banki ko P O S ba zai zarta naira Dubu 20 a Rana ba, da Kuma dubu 100 a mako ba Yayin da Suma kanfanoni ba zasu ciri sama da naira Dubu 500 a mako ba.

Matakin yasa Yan  Najeriya da dama kokawa

More from Labarai