On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Bankuna Zasu Fara Yiwa 'Yan Najeriya Katin Shaidar 'Dan Kasa Hade Da ATM - Pantami

Gwamnatin Tarayya ta ce a yanzu ‘yan Najeriya zasu iya neman bankunan kasuwancinsu su buga musu katin cirar kudi na ATM wanda zai iya aiki  matsayin katin shaidar zama dan kasa.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja.

Ya ce wannan bukata ta hade katin da lambara dan kasa kyauta ne.

Pantami ya ce an samu amincewar ne a taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce amincewar ta biyo bayan wata takarda da Hukumar Kula da Shaida dan  Kasa ta rubuta inda ta nemi a baiwa bankuna damar buga katunan cire  kudi da yawa wadanda zasu yi amfani amatsayin katin shaidar  kasa.