On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Bayan Wata 16 Kungiyar Kwallon Kafa Ta Wolves Ta Kori Mai Horaswa Bruno

Kungiyar kwallon kafa ta Wolves ta kori mai horas da 'yan wasanta  Bruno Large, sakamakon rashin nasara a hannun West Ham a gasar Premier a  ranar Asabar.

Wasa daya kacal kungiyar Wolves ta ci da rashin nasara a tara daga cikin wasanni 15 da ta buga a baya a gasar Premier, karkashin mai horaswar dan kasar Portugal.

Lage ya maye gurbin Nuno Espirito Santos ya kuma kai kungiyar mataki na 10 a kakar farko da ya ja ragama. sai dai Wolves ta ci kwallo uku kadai a bana da hada maki shida daga karawa takwas a gasar Premier.

Kungiyar ta kashe kudi sama da £100m wajen sayo 'yan wasa a kakar wasa ta bana, domin ta kara azama fiye da wadda ta yi a shekarar da ta gabata.

Ta dauko dan wasan Portugal, Goncalo Guedes da Matheus Nunes, kowanne kan £38m a matakin mafi tsada a kungiyar da ta saya a tarihi..

Wolves ta fada matsala, bayan Sasa Kalajdzic da Raul Jimenez suka ji rauni a kakar bana.

Magoya bayan kungiyar sun yi wa 'yan wasa ihu, bayan da West Ham ta doke Wolves a karshen makon jiya.