On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Bayern Munich Ta Lallasa Bercelona Da Ci 2 Da Nema A Gasar UEFA

Tambarin Bayern Munich Da Bercelona

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta yi wasan kura da kungiyar kwallon kafa ta Bercelona a Gasar UEFA da suka buga a daren ranar Talata.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta sake samun nasara a akan Barcelona inda ta doke ta da ci 2 da nema  a filin wasa na Allianz Arena.

 Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Mai buga gasar Bundesliga ta doke Barcelona daci 3 da nema a gida da waje a gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce.

Duka da cewar Kungiyar ta Bercelona ta taka rawar gani a mintuna 45 na farkon take wasan, sai dai Kungiyar ta Bayern Munich ta kwance mata zani a kasuwa yayin da Lucas Hernandez da Leroy Sane suka jefa kwallaye a ragar Kungiyar.

 Yanzu haka dai Kungiyar ta Bayern ta samu  nasara a wasanni biyu na rukunin C, Wanda Hakan yasa take gaban Inter Milan da Barcelona wadanda ke da maki uku.

More from Labarai