On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Bidiyo: An Bawa Gwamna Ganduje Sarautar Gargajiya a Birnin Badun

Mai martaba Olubadan na birnin Badun, Dr. Moshood Olalekan ya tabbatar da nadin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a matsayin Aare Fiwajoye na masarautar a ranar Asabar.

A cikin nadin da aka yi a yau, har da mai dakin Gwamnan Kanon, Hafsat Umar Ganduje, wacce ita ma aka nada ta a matsayin Yeye Aare Fiwajoye.

Sarkin ya ce an bawa Gwamna Ganduje sarautar ne bisa cancanta da kuma jajircewar sa wajen hidimtawa al'uma.

An gano manya-manyan kusoshin gwamnati da dama a wajen bikin nadin sarautar da aka gudanar a fadar Olubadan din dake birnin Badun.

Daga cikin wadanda suka halacci bikin akwai dan takarar shugaban kasar nan karkashin inuwar jam'iyyar APC a zabe mai zuwa, Bola Ahmad Tinubu.

Wani faifan Bidiyo da mai ba Gwamnan shawara na musamman kan al'amuran yada labarai, Abubakar Balarabe Kofar Na'isa ya wallafa a shafin sa na sada zumunta ya nuna Tinubu tare da Gwamna Ganduje yayinda suke wata gaisuwa irin ta al'ada.