On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Bola Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

TINUBU

Shugaban Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu, Ya baiyana dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairun 2023.

A lokacin da yake  baiyana  sakamakon zaben, Shugaban  hukumar  ta Inece  ya baiyana  cewa,  Asiwaju Tinubu  na jam'iyyar APC  ya samu kuri'a  Milyan   8 da  Dubu  794  da  726 , A yayin da  Atiku  Abubakar na jam'iyyar PDP Ya samu kuri'a  Milyan  6  da dubu  984  da 520  sai kuma  dan  takarar  shugaban kasa  na jam'iyyar  Labour  Peter  Obi, wanda yazo na ukku a zaben  da kuri'a Milyan 6 da dubu  101  da  533 A yayin da  Sanata  Rabiu Musa kwankwaso na jam'iyyar  NNPP  ya tashi  da kuri'a Milyan 1 da  dubu  496  da  687.