On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Buhari, Mataimakinsa, Gwamnoni 28 Da Kuma Ministoci Zasu Fara Bayyana Kadarorinsu Gabanin Karewar Wa’adin Mulkinsu

A yayin da wa’adinsu ke kara kusantowa, nan ba da jimawa ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa da ministoci 44 a majalisar zartarwa ta tarayya zasu fara bayyana kadarorinsu gabanin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Hakan ya fito ne daga bakin mai baiwa shugaban hukumar da’ar ma’aikata shawara, Dokta Mustapha Musa, wanda ya tabbatarwa manema labarai hakan a karshen mako, yace  akwai shirye-shiryen da suka dace domin bayar da fom din bayyana kadarorin ga jami’an da ke barin gado da kuma wadanda zasu  gaje su.

Haka kuma, hadiman shugaban kasa mai barin gado da gwamnonin jihohi 28 da ‘yan majalisar ministocinsu da  ‘yan majalisar dokoki ta kasa da na jiha da shugabannin kananan hukumomi za su karbi fom din bayyana kadarorin daga hukumar ‘Da’ar ma’aikata, sannan su mikawa ofishin kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 ya tanada.

Kundin tsarin mulkin kasar ya  yi tanadin cewa dukkan jami’an gwamnati za su bayyana kadarorin lokacin da zasu hau karagar mulki da kuma karshen wa’adinsu.

Sai dai zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da gwamnoni 28 masu jiran gado da mambobin majalisar ministocinsu da kuma ‘yan majalisar dokokin jiha nada watanni uku su mika fom din bayyana  kadarorin su ga hukumar ‘Da’ar ma’aikata.