On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Buhari Na Kowa Ne - Bola Tinubu

'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya taya shugaban kasa, Mohammadu Buhari murnar samun nasarar gudanar da zabukan fitar da gwani na jam'iyyar.

Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata wasika da tsohon gwamnan jihar Legas ya aikewa shugaban kasar, wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka kammala.

A cikin wasikar, Tinubu ya bayyana cewa, har zuwa ranar da za a gudanar da zabe, masu son tsayawa takara da sauran ‘yan Nijeriya suna jiran shugaban kasa ya bayyana   dan takarar da yake so.

Tinubu ya ce shugaban kasa ya ki ayyana kowa matsayin dan takararsa domin ya ba su dama mai kyau kamar yadda ya kamata a tsarin dimokuradiyya, ya ce hakika Buhari na kowa ne.

 

More from Labarai