On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Buhari Ya Halarci Bikin Yaye Sabbin 'Yan Sanda A Jihar Kano

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana kafofin Internet da sauran sabbin fasahohin zamani amatsayin manyan hanyoyin samar da tsaro da dakile laifuka.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a Ranar Alhamis  lokacin da yake gabatar da jawabinsa a bikin Ya ye 'Dalibai Karo na  hudu na 'Yan Sanda 205 na kwalejin 'yan sanda ta Kasa dake Kano, ya bayyana cewa a yanzu laifukan yanar gizo suna haifar da rashin tsaro. 

Najeriya, ta yi alkawarin ninka kokarin da take yi na takaita ayyukan ta'addanci da kai hare-hare a kasarnan. 

Buhari ya kara da cewa Najeriya ba za ta iya cimma nasara ba wajen yaki da rashin tsaro ba tare da tallafi da hadin kan kasashen makwabta ba. 

Sai dai kuma Buhari ya taya ‘yan Sabbi 'Yan Sandan murna, yayin da ya dora musu alhakin shiryawa domin tunkarar kalubalen da ke gabansu.

 Wakilin Bashir Faruk Durumin Iya ya Rawaito mana cewa, a nasa jawabin Shugaban Makarantar ‘yan sanda ta Kasa dake Wudil a Kano AIG Ahmad Abdurrahman ya ce kasafin kudin makarantar ba ya wadatarwa wajen gudanar da ayyukan da ake bukata da ke saukaka koyo da koyarwa, yana mai kira ga gwamnati da ta yi duba akan   kalubale.