On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Buhari Ya Kaddamar Da Kwalejin Sojojin Ruwa Da Sashen Tashi Da Saukar Jiragen Sama Na Kasashen Ketare A Kano

Shugaban Kasa Muhammadu Bihari, ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya.

Ayyukan sun hada da, bude kwalejin horas da  sojojin ruwa, a Karamar hukumar Dawakin Tofa ( Nigerian Navy Logistics college) sai katafaren gidan gyaran hali na Janguza da kuma gyara da aka yiwa filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano ( MAKIA) inda aka samar da sabon  Sashen Tashi Da Saukar Jiragen  Sama Na Kasashen Ketare

An kaddamar da wandan ayyuka ne ta allon-gani-ga-ka.

Shugaban ya yabawa gwamnan jihar da kuma hafsan sojin ruwa Vice Admiral AZ Gambo bisa kokarinsu na ganin an kammala aikin da kuma tabbatar da nasarar aiwatar da dukkan ayyukan.

A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Janar Bashir Salihi Magashi, ya ce  kwalejin ta yaye dalibai  sau biyu, kuma za ta yaye na uku a wata na shida nan gaba, inda ya ce kwalejin na neman sahalewa daga hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa domin a fara karatun  Diploma da shaidar HND a wasu kwasa-kwasai, inda farar hula zasu fara karatu a kwalejin.

Shi kuwa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa shugaban Kasar bisa wadannan muhimmanci ayyuka da shugaban Kasar ya gudanar a  jihar Kano.