On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Buhari Ya Karawa Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Wa'adi - Dingyadi

Ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Dingyadi, yace babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba, ba zai yi ritaya a tsakiyar babban zaben 2023 ba kamar yadda aka yi tsammani tun farko.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar gwamnatin tarayya bayan taron majalisar zartarwa na farko a shekarar 2023.

Dingyadi, ya ce tuni Baba ya samu takardar nadin da zai kara wa’adin aikinsa, ya kara da cewa dokar ‘yan sanda ta 2020 ta sauya ka’idojin ritayar Babban Sifetan ‘yan sanda.

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun nuna cewa Alkali Baba  zai cika shekaru 60 a ranar 1 ga watan Maris kuma ana sa ran zai mutunta dokar da ta umarci ma'aikatan gwamnati su yi ritaya daga shekaru 60.

Sai dai ministan yace bisa ga tanadin dokar 'yan sanda ta 2020, a yanzu babban siften ‘yan sanda zai rika cika wa’adin shekaru hudu akan mukamin daga lokacin da aka nadashi ba tare da la'akari da shekarunsa ba kuma tuni shugaban kasar ya ba shi takardar nadi a kan haka.

More from Labarai