On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Buhari Ya Nada Sabon Shugaban NYSC Wata Uku Bayan Tsige Birgediya Janar Fadah

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Birgediya janar Dogara Ahmed a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC).

Dogara zai karbi aikin ne a hukumance a yau Litinin 30 ga watan Janairu nan shekarar 2023 daga hannun Christy Uba, wacce ta rike mukamin na tsawon watanni kusan uku a matsayin mukaddashiyar darakta janar ta hukumar NYSC.

Uba, wacce itace babbar darakta a hukumar, fadar shugaban kasa ta nada ta amatsayin mukaddashiya mai kula da hukumar biyo bayan tsige Birgediya Janar Mohammed Fadah, bisa zargin rashin iya aiki a shekarr 2022.

A ranar 22 ga Nuwambar 2022, NYSC ta sanar da daukaka matsayin Christy Uba zuwa matsayin mukaddashiyar hukumar kula da shirin masu yi wa kasa hidima.