On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

CHANJIN KUDI : El-Rufa'ai Ya Umarci Mutanen Jihar Kaduna Su Cigaba Da Kashe Tsohon Kudi

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bijirewa matsayar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan manufar sake fasalin Naira, inda yace tsaffin takardun kudi na dubu 1 da Naira 500 da kuma 200 har yanzu suna aiki bisa doka a jihar.

Da yake yiwa ‘yan kasa jawabi a jiya Alhamis, Buhari ya umarci ‘yan Najeriya sumayar da  tsofaffin kudi na Naira 500 da dubu 1 zuwa rassan babban bankin kasa, yayin da tsohuwar takardar Naira 200 kawai ke  ci gaba da aiki bisa doka har zuwa 30 ga watan Afrilu.

Sai dai a jawabin da ya yi ga al’ummar  jihar a daren jiya, El-Rufai yace takardun kudin suna nan a kan doka har sai kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin akasin haka.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffi da sabbin takardun kudi ba tare da wani tsoro ba.

Ya yi zargin cewa karancin kudin Naira wata makarkashiya ce ta haifar da hargitsi da kuma kafa gwamnatin wucin gadi a Najeriya.