On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

CHANJIN KUDI: Tsohuwar Takardar Naira 200 Ce Kawai Zata Cigaba Da Aiki Tare Da Sabbin Kudi Zuwa Kwanaki 60 A Najeriya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace tsohuwar  takardar  kudi ta Naira 200 na nan a matsayin halartaccen kudi na doka har zuwa ranar 10 ga watan  Afrilu na shekarar da muke ciki ta 2023.

Yace ya umurci babban bankin kasa CBN da ya saki tsofaffin takardun Naira 200 domin su cigaba da zagayawa kamar yadda doka ta tanada, inda za’a cigaba da amfani da kudin tare da sabbin takardun kudi na Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira dubu 1 na tsawon kwanaki 60 daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan a yayin gabatar da jawabi ga ‘yan kasa, ya ce an dauki wannan matakin ne domin saukaka wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki a sakamakon wannan sabon tsari na harkokin kudi.

Shugaban ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bibiyar  yadda ake aiwatar da tsarin da nufin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya ba su shiga mawuyacin hali ba.

Yace CBN zai  tabbatar da cewa sabbin takardun kudin wadata  ga ‘yan kasa ta hanyar bankuna.

Sai dai shugaba Buhari ya bayyana cewa ya umarci babban bankin ya kara karfafa hadin gwiwa da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda za a tabbatar da cewa an dauki matakin doka kan duk wani bangare na kamfani ko hukuma ko mutanen da aka samu da kawo cikas ko yin zagon kasa a aiwatar da tsarin.