On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Cikin Shekara Biyar An Sace 'Danyen Mai Na Trilliyan 4.3 A Najeriya - NEITI

Hukumar da ke binciken yadda aka kashe kudaden da aka samu daga ma'adanan man fetur a Najeriya, NEITI,, ta ce an sace danyen mai  na  sama da Naira trilliyan 4.3 a hare-haren fasa bututun mai guda dubu 7 da 143 a cikin shekaru biyar.

Babban sakataren zartaswa na hukumar, Ogbonnaya Orji ne ya bayyana hakan a taron fasahar bututun mai na kasa da kasa da aka yi a Abuja ranar Litinin.

Orji ya ce satar mai wani al’amari ne na gaggawa da ke haifar da babbar barazana ga hako man fetur da kuma yin amfani da shi tare da babbar illa ga ci gaban tattalin arziki da kasuwanci na kamfanonin mai.

Ya yi zargin cewa da yawa daga cikin ‘yan kungiyar dake harkokin bututun mai suna da hannu kai tsaye da kuma a fakaice wajen samar da kwarewa da ilimin da ake bukata wajen satar mai.