On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

CIRE TALLAFIN MAN FETUR : Najeriya Ta Adana Trilliyan 1.45

Gwamnatin tarayya ta yi tsumin  kusan Naira trilliyan 1.45 daga kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur tsakanin watan Yuni zuwa Satumba.

Wannan ya zo ne bisa ga takardun kwamitin Tarawa da rabon arzikin kasa da aka samu daga shafin yanar gizon Gwamnonin Najeriya da Ofishin Kididdiga na Kasa.

Wani bincike ya nuna cewa kudaden da ake aikawa duk wata zuwa asusun ajiyar kudaden da ba na man fetur ba na gwamnati sun kai billiyan 696.93 a watan Yuni, da billiyan 389.7 a watan Yuli sai billiyan 71 a watan Agusta da kuma billiyan 289 a watan Satumba.

Kafin cire tallafi dai, kamfanin man fetur na Najeriya ya ce ya kashe Naira trilliyan 1.828 wajen biyan tallafin daga watan Janairun 2023 zuwa Mayu 2023,  kashi 55 cikin dari fiye da adadin da aka biya a daidai lokacin a shekarar 2022.