On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Cutar Amai Da Gudawa Da Sankarau Sunyi Ajalin Mutum 88 A Najeriya - WHO/NCDC

Wani rahoton hukumar lafiya ta Duniya, ya nuna cewa kimanin mutum 922 ne suka kamu da cutar amai da gudawa a Najeriya, sai mutum 32 suka mutu sakamon cutar a shakerar da muke ciki ta 2023.

WHO ta ce  zuwa 5 ga watan Maris da muke ciki na 2023 yawan mace-mace sakamakon cutar ya kai kashi 3.5 cikin 100

Hukumar lafiya ta duniya ta kuma ce alƙaluman sun haɗar da waɗanda suka bayyana alamun cutar, da kuma waɗanda aka tabbatar da cewa sun kamu a ɗakunan gwajin cutar da ke asibitoci.

Ana hasashen alkalouman za su iya sauyawa a kowanne lokaci sakamakon rahotonni da ake samu a mabambantan wurare a faɗin ƙasarnan.

Ita kuwa cibiyar daƙile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta ce an tabbatar da mutum 157 da ke ɗauke da cutar sankarau tsakanin watan Oktoba na 2022  zuwa watan Maris da muke ciki na 2023.

Haka kuma an samu mutum 628 da ake zargin sun kamu da cutar, ciki har da mutum 52 da suka mutu a jihohi 21.