On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Da 'kudin aljihuna na yi tallafin Tukwane da Likafani - Sanata Hanga

Sanatan Kano ta tsakiya Rufa'i Sani Hanga  ya ce tallafin tukwane da Likafani da kuma Motocin daukar Gawa taimako ne na kashin Kansa ba aikin mazaba ba.

Sanata Hanga ya ce tallafin anyi shi ne  saboda Allah da kuma aikin Alkhairi da ya saba gani tun daga gidansu.

Sanata Hanga, dan jam'iyyar NNPP ya fuskanci martani bayan tallafin kayan binne mamata. 

Da yake tabbatar da dalilin bayar da tallafin,  Sanata Hanga ya tabbatar da cewa tallafin ba ya cikin ayyukan mazabar sa, sabanin rahotannin da ake yadawa.

Ya kuma jaddada cewa irin wadannan ayyukan na sadaka ba sabon abu bane a gare shi, inda ya bada misali da abun da ya gada kuma yake  ci gaba da aiwatarwa a rayuwarsa. 

A taron manema labarai na farko da ya yi tun bayan zabensa a shekarar 2023, Sanata Hanga ya yi karin haske kan muhimmancin tallafin.

Ya bayyana cewa an bayar da tallafin ne ga kwamitin makabartu na jihar Kano, karkashin jagorancin Sarkin fadar Kano da hakimin Tarauni.