On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kawar Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji daga arewa maso yamma da ke aiki a jihar Zamfara sun kashe wasu ‘yan bindiga da dama da suka yi yunkurin kai hari kauyen Karazau da ke karamar hukumar Bungudu a jihar.

Wata majiya mai tushe da ke kusa da rundunar ta sanar da jaridar PUNCH cewa dakarun sun amsa kiran da aka yi musu na gaggawa a kan lokaci game da  ‘yan ta’adda da suka kai hari kauyen Karazau a ranar Asabar da ta gabata.

A cewar majiyar, yayin da suke tunkarar kauyen, ‘yan ta’adda dauke da makamai sun yi wa sojojin kwanton bauna.

Sai dai a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai garin Maru shalkwatar karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum hudu ciki har da wani malamin kwalejin ilimi ta Maru, Dr Nasiru Anka.

Wani dan yankin mai suna Mohammed Bawa ya shaidawa jaridar PUNCH cewa ‘yan bindigar sun kai hari garin Maru a daren ranar Asabar, inda suka kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da wasu mutum hudu ciki har da wani malami a Kwalejin Ilimi ta Maru.