On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

‘Daliban Kano Dubu 15 Ka Iya Rasa Damar Rubuta Jarabawar NECO Saboda Bashin N1.5 Billiyan

Akalla ‘Daliban jihar Kano da adadin su ya kai dubu 15 ka iya rasa rubuta jarrabar kammala sikandire ta NECO a wannan shekarar, wadda za a fara a Yau, sakamakon bashin da hukumar ke bin gwamnatin jihar ta Kano, wanda ya kai kimanin naira biliyan daya da Rabi.

Hukumar dake shirya jarrabawar ta yi alwashin daliban jihar ba za su rubuta jarrabawar ba, sakamakon yawan bashin da take bin gwamnatin jihar.

Babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Hajia, Lauratu Ado, ta tabbatar da hakan, inda tace yanzu haka gwamnatin na tattaunawa da hukumar ta NECO.

Ta ce gwamnatin jihar Kano ta biya Neco naira miliyan 356 a makon daya gabata, sai dai hukumar tace sai an biyata miliyan 700, ta kara da cewa gwamnati ta bada miliyan 300, wanda ma’aikatar ilimi ta baiwa hukumar a jiya, sai dai har yanzu bata bude shafin nata ba, wanda ake fatan biyan kudin zai  kammala zuwa Yau.