On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Daliban Makarantun Abuja Sun Rubuta Jarabawar Darussa 13 A Rana Daya Saboda Barazanar Rashin Tsaro.

DALIBAI NA RUBUTA JARABAWA

Biyo bayan barazanar da ‘yan bindiga suka yi na kai hari Makarantar Koyon aikin shari’a ta kasa dake Kwali a birnin taraiyya Abuja, A yanzu haka Ma’aikatar Ilimi ta kasar bayar da umarnin rufe dukkan makarantun da ke Abuja babban birnin taraiyyar Najeriya.

Umurnin ya zo ne a daidai lokacin da dalibai ke rubuta jarabawar zango na uku, kuma a wani mataki na cika umarnin da ma’aikatar ilimi ta bayar, Hakan tasa Hukumomin makarantun suka yi gaggawar kammala rubuta  jarabawar da tayi saura ga daliban.

Wani dalibin  karamar Sakandire  ta  Kubwa da ke Abuja, ya koka kan yadda malamansu suka sa su rubuta jarabawar  darussa 13 a ranar Talata.

Dalibin ya ce wasu daga cikinsu sun  razana, saboda fargabar  yiwuwar kai  masu harin  ta’addanci. Mazauna Abuja sun shiga cikin fargaba sakamakon karuwar masu satar mutane da kuma  harin  kwanton bauna da aka  yiwa wasu sojoji a karshen makon jiya.

 

More from Labarai