On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Dalibin Jami'ar Wudil a jihar Kano ya samar da Risho Mai amfani da Ruwa

Abuja, inda ya nuna Fasahar da ta zama cikin wadanda sukayi fice a gasar

 

Wani ‘Dalibi dan asalin jihar Kano ya hau kan turbar samarwa ‘yan Najeriya mafita daga kalubalen makamashi 
 biyo bayan wahala da tsadar Kalanzir da gas din girki..

‘Dalibin Yusif  Shamsudeen na  Jami’ar kimiyya da Fasa ta Kano dake garin Wudil ya samar da wata Fasahar Risho mai amfani da Ruwa..

A baya bayan nan ‘Dalibin Yusif ya wakilci jami’ar a gsar baje kolin fasahar kirkire-kirkire ta kasa da hukumar kimiyya da Fasaha ta kasa ta shirya a Abuja, inda ya nuna Fasahar da ta zama cikin wadanda sukayi fice a gasar..

Yayin bikin kaddamar da wannan Fasahar makamashin griki ranar Laraba, shugaban Jami’ar kimiyya da Fasaha ta Kano dake Wudil Farfesa Shehu Alhaji Musa, yace nan bada jimawa ba Jami’ar zata fara cinikayyar sabon Risho din girkin mai amfani da Ruwa.