On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Dan Chinan Nan Ya Musanta Zargin Halaka Marigayiya Ummita

Marigayiya Ummita da Dan China

Dan'asalin Kasar China nan, mai suna Geng Quanrong da ake zargi da Kisan Ummakulsum Sani Buhari a Unguwar Janbulo dake Jahar Kano bayan caka mata wuka ya musanta zargin da akai masa na Kisan Kai a gaban Kotu.

A zaman Kotun me lamba 17 dake Miller Road Karkashin Sunusi Ado Ma'aji a Yau, Babban Lauyan Gwamnati Barr Musa Abdullahi Lawal ya roki Kotun ta Karanta masa Kunshin tuhumar da ake masa, bayan karanta masa ne nan take ya musanta.

Daga nan sai Lauyan Gwamnati ya nemi a basu wata rana domin su kawo shaidunsu gaban  Kotun ta sanya ranar 16 da 17 da kuma 18 ga watan Nuwambar 2022 domin cigaba da sauraron karar.

Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya wanda yaje kotun, ya labarta mana cewa wani Dan'asalin Kasar China Mr Guo Cunru ya bayyana a gaban Kotun a matsayin me yiwa Geng Quanrong Tafinta kamar yadda Kotun ta umarta a zamanta na baya.