On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Dan Fansho Ya Yanke Jiki Ya Fad'i Suna Tsaka Da Zanga-Zangar Neman Hakokinsu A Hannun Gwamnatin Jihar Kano

Wani dan fansho da ba’a baiyana sunansa ba, ya yanke jiki ya fadi lokacin da ake tsaka da gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna takaici kan kin biyansu hakkokinsu na Gratiutie da sauran wasu hakkoki bayan kammala aikin gwamnati.

Bayan faruwar al’amarin an dauki dan fasnshon zuwa Asibiti mafi kusa domin bashi kulawar gaggawa.

Wakilinmu Victor Chiristopher wanda ya halarci wurin da ‘yan fanshon suka gudanar da zanga-zangar, ya gansu dauke  da kwalaye  wadanda aka yiwa rubuce-rubuce daban daban, wanda ke cewa’’’ a biya mu hakkokinmu na Ariyas, A biya mu hakkokin ma’aikatan da suka mutu, Yan fansho na mutuwa, A yi aiki da dokar Fansho ta shekarar  2006 da sauransu.

Da yake jawabi a madadin masu zanga-zangar, Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, kwamared Kabiru Ado Minjibir, Ya Koka da cewar a cikin shekaru biyu da suka gabata an cire sama da naira biliyan ukku  daga cikin hakkokin  ma’aikatan da suka yi ritaya  na wata-wata da ake biyansu.

“Daga watan Janairu na shekarar 2021 zuwa Agusta na 2022, an cire Naira billiyan 2 da milliyan 573 da dubu 949 da kwabo 61  daga kudaden  ‘yan fansho na kananan hukumomi. Kuma daga Maris na 2021 zuwa Agusta na 2022, an cire milliyan 906 da dubu 917 da 595 da kwabo 17 daga ‘yan fansho na jiha.

Sai dai Kwamared Minjibir ya bukaci gwamnatin jihar da ta magance matsalolin da ‘yan fansho ke ciki a jihar domin ceto asusun fansho na jihar daga durkushewa.

"Muna kira ga Gwamnatin Jihar da ta magance matsalolin mutanen  da suka yi ritaya daga yankar musu kudade.

Da yake mayar da martani, gwamnan jihar Kano,  Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata na jihar, Dr Usman Bala, yace gwamnati ta dauki kwararan matakai na magance matsalolin da ‘yan fansho ke fuskanta a jihar ta Kano.

“Batun yankarwa ma’aikatan da suka yi ritaya kudadensu an fara ne a zamanin gwamnatin da ta gabata. Amma duk da haka, za mu dauki karin ma’aikata dubu 1 don magance matsalar.