On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

'Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar PDP A Najeriya Ya Sake Yin Tuntuben Harshe A Jihar Kogi

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sake fuskantar tuntuben harshe a lokacin yakin neman zaben jam’iyyar a jihar Kogi.

A taron da aka gudanar a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, Atiku Abubakar ya nemi magoya bayan ‘yan jam’iyyar su zabi APC, kafin daga bisanin yayi gaggawar  gyarawa yace PDP.

Hakan na zuwa ne  makonni bayan Atiku Abubakar ya yi irin wannan tuntuben harshe a lokacin yakin neman zaben jam'iyyar a filin wasa na Rwang Pam da ke Jos, babban birnin Plateau.

Abubakar, wanda a baya ya koma jam’iyyar APC, ya sake komawa PDP ne a watan Disambar 2017.