On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Dan Wasa Victor Osimhen Ya Zama Na Ukku A Jerin Yan Wasa Mafi Kwazo A Duniya Yan Kasa Da Shekara 25

DAN WASA VICTOR OSHIMEN

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Napoli da kuma Super Eagles, Victor Osimhen, ya kasance a matsayi na uku a cikin jerin yan wasan gaba yan kasa da shekaru 25 a duniya da suka fi kwazo.

Kididdigar da hukumar kula da kwallon kafa ta CIES ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata, ta nuna cewa dan wasan ya samu cigaba da mataki na shida zuwa  matsayi na Ukku, bayan day a samu maki 93 da digo 3.

Shi kuwa dan wasa Kai Havertz na Chelsea ya shine dan wasan gaba  na farko mafi kwazo inda yake da maki 94 da digo 3, a yayin da dan wasan gaba na Atletico Mineiro Matias Zaracho ya kasance a matsayi na biyu da maki 93 da digo 4.

Dan wasa Osimhen dake da  maki 93 da digi 3 ya yi kan-kan kan, da dan wasa Ferran Torres na Barcelona wanda  yake a matsayi na Hudu.

More from Labarai