On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

DCP Abba Kyari Ya Na Neman Kotu Tayi Watsi Da Karar Da Hukumar NDLEA Ta Shigar Akansa

Dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari ya kalubalanci ikon hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA na gurfanar da shi gaban Kotu.

Kyari na fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume takwas na safarar miyagun kwayoyi.

A zaman da aka yi a jiya, Kyari, ta hannun lauyansa, Nureni Jimoh, ya gabatar da cewa tuhumar da ake masa ba ta da tushe balle makama.

Yace ba’a kammalabinciken ‘yan sanda ba akan  laifin da ake tuhumarsa, ya kara da cewa ya kamata hukumar ta NDLEA ta baiwa ‘yan sanda damar kammala bincike da kuma matakin ladabtarwa na cikin gida kafin ta shigar da kara a kansa.

Kyari ya cigaba da cewa hukumar ‘yan sanda tana da irin wannan iko na ladabtar idan jami’an ‘yan sanda da suka yi kuskure, kamar yadda majalisar koli kan harkokin shari’a ta kasa  ke ladabtar da jami’an shari’a.

Sai dai ya bukaci kotun da ta yi watsi da tuhumar ta kuma sallame shi.