On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Direbobin Tankar Dakon Fetur Na Barazanar Ballewa Daga Kungiyar NUPENG

Kungiyar direbobin tankokin mai karkashin kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, tayi barazanar ficewa daga kungiyar NUPENG.

Kungiyar direbobin ta ce  za ta fice daga kungiyar idan shugaban NUPENG na kasa, Williams Akporeha, da babban sakatarenta, Olawale Afolabi, suka gaza sauka daga kan mukamansu.

Direbobin tankar sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a Abuja tare da sanya hannun Gbenga Olawale da Adekunle Rufa'I dake shugabantar Depo na  Ibadan.

Sanarwar ta ce direbobin sun gudanar da zanga-zangar a fadin kasarnan, inda suka nuna kwalaye da ganye a gaban manyan motocinsu, sannan kuma sun gargadi kungiyar ta NUPENG da ‘yan sanda kan tsoma baki da cin zarafin shugabanninsu.