On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Dole Mu Kalubalanci Duk Wani Yunkuri Na Kuntatawa 'Yan Najeriya - NLC,TUC

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi barazanar daukar mataki a hannunta biyo bayan karin farashin man fetur.

Kungiyar ta NLC a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugabanta na kasa Joe Ajaero, ta zargi gwamnatin Tinubu da tatse talakawa domin hidimtawa masu hannu da shuni da kuma jefa  ‘yan Najeriya cikin wahala.

Ya kuma yi nuni da kudirin biyan ‘yan majalisar dokokin kasarnan zunzurutun kudi har naira biliyan 70 da Naira billiyan 36 ga bangaren Shari’a yana maibayyana hakan amatsayin  mafi girman karkatar da kudade cikin aljihun jami’an gwamnati.

Ita kuwa, kungiyar kwadago ta TUC ta bakin mataimakin shugabanta na kasa, Tommy Etim, ita ma ta caccaki gwamnatin tarayya kan karin farashin man fetur, inda ta ce yanzu kasarnan na fuskantar rudanin tattalin arziki.