On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

DSS Ta Musanta Rahotannin Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce rahotannin da ke ikirarin cewa jami’anta sun mamaye babban bankin kasa CBN domin kama gwamnan banki, Godwin Emefiele, ba gaskiya ba ne.

A ranar Litinin dai  aka samu rahotanni a kafafen sadarwa na Internet cewa hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta kai simame shalkwatar CBN domin kama Emefiele bisa zargin aikata laifukan daukar nauyin ta'addanci.

Sai dai a wata sanarwa da Peter Afunanya, mai magana da yawun DSS ya fitar, hukumar ta musanta wannan ikirarin, inda ta ce rahoton yaudara ce kawai.

Idan za’a iya tunawa ana ta samun takaddama a tsakanin hukumar DSS da Emefiele kan zargin gwamnan babban bankin da daukar nauyin yan ta’adda.

DSS dai a baya ta shigar da kara dake bukatar kotu ta umarci a kama Emefiele, sai dai kuma kotun tayi watsi da bukatar, sannan kuma ta haramta kama ko gayyata ko kuma tsare Emefiele.

Emefiele dai ya shafe tsawon lokaci baya Nigeria sakamakon hutu daya dauka, amma ya dawo Najeriya  bayan hutun  inda ya fara aikinsa a ranar Litinin.

More from Labarai