On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Duk Wanda Bai Kawo Akwatunsa A Zaben Gwamnan Jihar Kano Ba Yana Ruwa – Rarara Ya Gargadi Masu Rike Da Mukamai

Shugaban kungiyar 13x13 a Najeriya Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, ya gargadi jagorori da masu rike da mukamai a karkashin gwamnatin jam’iyyar APC da cewa duk wanda ya gaza yin nasarar zaben gwamna a akwatunsa kar ya sa rai da sake samun gurbi a sabuwar gwamnati.

 

Rarara ya yi wannan gargadi ne a wata zantawa da manema labarai a Kano, yace a wannan zaben na 2023 ga zaben Bola Tinubu ga kuma na Gawuna duk wanda bai ci akwatunsa ba bai kawo mazabarsa ba yana ruwa.

13x13 kungiya ce ta shahararrun mutane masu fasaha da suka yi fice a fannin nishadantar da al'umma musamman a arewacin Najeriya, a makon jiya anji yayi wata waka mai taken girmanka akwatunka.

Rarara wanda kuma shine shugaban mawakan jam’iyyar APC na kasa, yace raini ne wadanda suka gaza cin zaben jam’iyyar a akwatunsu su je neman samun mukami ko samun wajen zama a gwamnati.

Ya yi zargin cewa ana kyale wasu suna yin yadda suka ga dama a wajen akwatu sabaoda rashin samun wadanda zasu tsaya kai da fata.

Yace a yanzu ko kwamishina ko shugaban karamar hukumar ko shugaban jam’iyya ko sakataren karamar hukuma ko shugabannin ma’aikatu da hukumomi da Kansila dole ne sai sunyi nasara a akwatunsu kafin sa rai da matsayi.

More from Labarai