On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

EFCC Na Bincike Kan Tsaffin Gwamnoni Da Ministoci Da Kuma Jami'an Gwamnati A Najeriya

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta ce wasu tsofaffin gwamnoni da  tsofaffin ministoci da wasu jami’an ma’aikatu suna fuskantar bincike kan wasu korafe-korafe da hukumar ta samu akansu.

Kakakin hukumar,  Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da hakan a ranar Laraba, ya ce nan ba da dadewa ba za a fitar da bayanai kan cikakken.

Oyewale ya kuma bayyana cewa hukumar EFCC ta kwato naira biliyan 27 da dala miliyan 19 a wasu shari’o’i uku da ta gudanar da bincike, inda ya kara da cewa kudaden da aka ware domin ayyukan wutar lantarki na Mambilla da Zungeru ana karkatar da su ne ta hanyar wasu  ‘yan chanji.

A cewarsa, yanzu haka ana ci gaba da kwato gidaje da dama da aka saya da kudaden a Abuja da  Legas da kuma jihar Cross River.