On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

EFCC Ta Kama Masu Sayen Kuri’a A Zaben Jihar Ekiti

Hukumar da ke yaƙi da masu yiwa Arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ta kama wasu mutane da ake zargi da sayen ƙuri'u a yayin zaɓen gwamna a jihar Ekiti.

Hukumar EFCC na cikin hukumomin tsaro da suka aike da Jami'ansu domin Sanya idanu kan yadda zaben ke gudana.

Anyi holen wasu daga cikin mutanen da ake zargi a offishin 'yan sanda na Oke Ori Omi bayan an kamasu da ake zargin suna amfani da su Wajen sayen Kuri'a.

Haka Kuma Jami'an na EFCC sun yi dirar mikiya a wata rumfar zaɓe inda suka yi awon gaba da wasu, sannan an kama wasu mutane a wani gida suna amfani da Littafi wajen lissafa bayanan masu zabe a wani yanki na Jihar.

Dama tun da safiyar  ranar asabar wasu daga cikin masu jefa ƙuri'a suke ta kokawa kan yadda suka ce ake sayen ƙuri'u a wasu rumfuna zaɓe.

Wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna yadda jami'an EFCC suka yi dirar mikiya a wata rumfar zaɓe inda suka yi awon gaba da wasu.