On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Fadar Shugaban Kasa Ta Mayar Da Martani Ga Peter Obi Kan Hukuncin Kotun Koli

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani gad an takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, inda ta ce Obi ya taba cin gajiyar hukuncin kotu a shari’ar da akayi lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Anambra a shekarar 2007.

Fadar shugaban kasar ta ce abun mamaki ne yadda  yanzu shi Obi ke  sukar bangaren shari’a a lokacin da Kotun Koli ta yanke hukunci a kan zaben Shugaba Bola Tinubu a ranar 26 ga Oktoba na  2023.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa sa’o’i bayan Obi ya caccaki hukuncin kotun koli wanda ya tabbatar da nasarar zaben Tinubu, dan takarar jam’iyyar APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Onanuga ya ce ya kamata Obi da jam’iyyarsa su sani cewa kotun koli ko wata kotu ba ta bayar da hukunci bisa ra’ayiko bukatar wani.