On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Farashin Gangar Danyen Man Najeriya Ya Tashi Zuwa Dala 100 A Kasuwar Mai Ta Duniya

Gangar Danyen Mai

Kungiyar kasashe masu arzikin fitar da mai ta duniya OPEC da kuma kawayenta, sun amincewa Najeriya ta rika hako ganga Milyan 1 da dubu 80 a kowace rana tun daga farkon watan satumbar bana.

Najeriya na hako ganga Milyan 1 da dubu 826 ne a kowace rana a cikin wannan wata na Augusta, Sai dai kungiyar ta Opec ta baiyana cewa sabon matakin zai temaka wajen inganta farashin kasuwar danyen mai a duniya.

Jim kadan bayan sanarwar ne, Farashin danyen mai samfurin na Najeriya ya tashi zuwa Dala 100 akan kowace ganga daya.

Sai dai kuma masu sharhi na kallon da wuya kasar nan ta iya cimma wannan alkaluma a kowace rana, wanda a yanzu haka bata iya hako sama da ganga milyan 1 da dubu 400 a kowace rana, sakamakon satar danyen mai da kuma fasa bututan da ake yi.

More from Labarai