On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Farashin Man Jiragen Sama Da Iskar Gas Sun Karye A Najeriya

Farashin man jiragen sama da aka fi sani da Jet A1 ya sauka jim kadan bayan an cire tallafin mai wanda ya yi tashin gwauron zaɓi.

Rahotanni na cewa daga sama da Naira 800, man jirgin ya sauka zuwa Naira 650 a Legas da kuma Naira 680 a Abuja daga ranar 1 ga watan Yuni yayin da ya dan fi haka a Kano da Maiduguri da Fatakwal.

Hakan abun yake da iskar gas din girki mai nauyin kilogiram 12.5 wanda farashin ya karye daga kimanin Naira dubu 14 zuwa Naira dubu 6 da 950 a Legas da kuma kimanin Naira dubu 8 a wasu jihohi kamar yadda aka gani a jiya.

Binciken da aka yi a wurare daban-daban a jiya ya nuna cewa ana siyar da iskar gas din akan Naira 700 zuwa 800 kan kowanne kilogiram daya sabanin Naira dubu 1 a makonnin baya.

More from Labarai