On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Fasinjoji 20 Sun Kone A Sakamakon Hadarin Mota A Jihar Oyo

HADARI

Kimanin fasinjoji 20 ne suka kone a sakamakon wani kazamnin hadarin mota wanda ya faru akan shatale-talen Maya zuwa Lanlate dake karamar hukumar Ibarapa ta Gabas a jihar Oyo.

Rahotanni na baiyana cewa  hadarin ya ritsa da  wasu motoci biyu inda suka yi taho-mu-gama da juna  wanda a nan take suka kama da wuta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Ibarapa ta Gabas, Mista Gbenga Obalowo, ya ce shi ne ya jagoranci tawagar  jami’ain aikin ceto zuwa inda hadarin ya faru, inda ya jajantawa iyalan wadanda abun ya ritsa dasu.

Sai dai kuma, Har yanzu ba’a kaiga jin tab akin  kwamandan hukumar kare afkuwar haddura na  jihar Oyo, Joshua Adekanye, sakamakon rashin amsa kiran waya da kuma sakwannin kartakwana da aka tura masa.

 

More from Labarai