On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Firiministar Burtaniya Tayi Murabus

Liz Truss Tayi Murabus Daga Muƙaminta Firaministar Birtaniya, Kwanaki 45 Bayan Kama Aiki.

Ƴan majalisar dokokin kasar na jam'iyyar masu ra'ayin rikau sun buƙace ta da ta sauka daga  mulki bayan da gwamnatin ta ta ci karo da matsaloli.

Ajiye muƙamin na zuwa ne bayan da wata minista ta ajiye aikinta ranar laraba, yayin da ƴan majalisa na jam’iyyar Conservatives suka yi mata bore.

A watan Satumba na 2022 aka zaɓi Truss a matsayin firaminista, sai dai kwarjininta ya ragu bayan soke wasu daga cikin manufofi da ta ɓullo da su.